1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rukunin da ke sasantawa a rikicin Gabas Ta Tsakiya ya yarje kan wani shiri na tallafa wa Falasɗinawa.

June 18, 2006
https://p.dw.com/p/ButU

Ƙasashe da kafofin rukunin nan da aka yi wa laƙabin ’yan huɗu, mai yunƙurin sasanta rikicin Gabas Ta Tsakiya, sun yarje kan wani shiri na talllafa wa Falasɗinawa, ba tare da bi kan gwamnatin da Ƙungiyar Hamas ke jagoranta a halin yanzu ba. Rukunin dai na yi wa Ƙungiyar Hamas ɗin saniyar ware ne, saboda dagewar da take yi ta ƙin amincewa da wanzuwar Isra’ila tamkar ƙasa. A cikin wata sanarwar haɗin gwiwar da suka bayar, Amirka, da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, da Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Rasha, waɗanda su ne mambobin rukunin, sun ce sun yarje da wata shawarar da Ƙungiyar EU ta gabatar, wadda ta tanadi wani shiri na wucin gadi, inda rukunin zai ba da taimako ga kafofin kiwon lafiya da na kula da halin rayuwar jama’ar Falasɗinawan kai tsaye, ba tare da tallafin ya shiga hannun Ƙungiyar Hamas ba. Sun dai yi kyautata zaton cewa, masu ba da taimako na ƙasa da ƙasa, a cikinsu har da Isra’ila, su ma za su ba da tasu gudummowa ga shirin.

Tun da Ƙungiyar Hamas ta hau kan karagar mulki ne, aka katse mafi yawan taimakon ƙasa da ƙasa da ake bai wa yankunan Falasɗinun. Amirka da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai dai nqa ganin Ƙungiyar ta Hamas ne tamkar ƙungiyar ’yan ta’adda.