1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar Eufor ta yi kira a daina zanga-zanga a DRC

September 19, 2006
https://p.dw.com/p/Buix

Rundunar Eufor, da ƙungiyar taraya turai ta aika a jamhuriya Demokradiyar Kongo, ta yi kira ga hukumomin ƙasar da su ɗauki matakan dakatar, da zanga zangar da ta ɓarke tun jiya birnin Kinshasa.

A yammacin jiyan ne, gidan talbajan mallakar maitamakin shugaban ƙasa , Jean Pierre Bemba a Kinshasa ya kone kurmus, a cikin wata gobara, da har yanzu, ba a gane mussabbabin ta ba.

Magoya bayan ɗan takara Jean Pierre Bemba, na zargin ɓangaren shugaban ƙasa Joseph kabila, da cinna wutar da gangan.

Rundunar Eufor ta bukacin bangarorin 2, sun ladabtar da magoya bayan su, don kauce kasar faɗawa cikin wani saban rikici, a lokacin da ake shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na 2.