1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar Isra´ila ta janye daga yankin Beit Hanoun

November 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bud2

Rundunar Isra´ila ta bayyana hita daga yankin Beit Hanoun na zirin Gaza, da ta mamaye a tsawan kwanaki 6.

Rundunart a kai hare-hare masu yawa, a wannan yanki, wanda su ka hadasa mutuwar Palestinawa kimanin 60.

Isra´ila, ta kai wannan hari, da zumar capke wasu sojojin ƙundumbala, na ƙungiyar Hamas, da ke shirin harba rokoki.

Ministan harakokin tsaron Isra´ila, Amir Perez, ya bayana gamsuwa da wannan hari, wanda yayi nasara ƙwato rokoki masu yawa, da kuma capke yan ƙunar bakin waƙe da dama.

Ƙasashe daban-daban na ƙetare, sun yi Allah wadai da harin.

Shikuwa ministan tsaron Palestinu, Mahmud Zahr, kira yayi ga kasashen larabawa, sun ba shi, tallafi cikin gaggawa domin fuskantar wannan al´amari.

A ɗaya hannun kuma, shugaban hukumar Palestinu Mahamud Abbas, da Praminsita Isma´il Hanniey, sun shirya zaman taro na mussamman, da burin kai ga nasara girka gwamnatin haɗin kann kasa, saidai taron ya watse baran-baran.