1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar Isra´ila ta kai hare-hare ga wasu yankunan Palestinawa

May 30, 2006
https://p.dw.com/p/BuwA

Rundunar tsaraon Isra´ila ta kai hare hare ga yankunan zirin Gaza, da yammacin kogin Jordan, inda ta hallaka Paletinawa a ƙalla 7, tsakanin daren jiya, zuwa yau da sahe.

Tun bayan da dakarun Isra´ila su ka fita daga wannan yankuna a shekara da ta gabata, wannan shine hari mafi muni, da su ka ƙaddamar.

Isra´ila ta bayyana wannan mataki, a matsayin maida martani, ga rokokin da yan Jihadil Islami, su ka harba, zuwa ƙasar ta bani yahudu.

Kakakin rundunar tsaron Isra´ila, ya sanar cewa, za su cigaba da kai wannan hare hare, a duk lokacin da ya dace, domin kare Isra´ila, daga yan ta´ada Palestninu.

Ƙungiyar Jihadil Islami, ta yi asara 3 daga shugabanin ta, a cikin harin, da su ka haɗa da, Mohamed Matter, Mohamad Abou Shanab, da kuma Youssouf Abou Naza.

Wannan rikici, ya ɓarke, a yayin da ake shirye shiryen ganawa a watan juni mai zuwa, tsakanin shugaban hukumar palestinawa Mahamud Abbas, da saban Praministan Isra´ila Ehud Olmert.