1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar Libanon ta sa kafa kudancin ƙasar.

Yahouza S.MadobiAugust 17, 2006

Karo na farko bayan shekaru 40 da su ka gabata,sojojin Libanon sun sa ƙafa a kudancin ƙasar.

https://p.dw.com/p/Btyg
Hoto: AP

Kwanaki 5, bayan lafawar yaƙi , tsakanin dakarun Isra´ila da na Hizbullahi, gwamnatin ƙasar Libanon ta fara aika dakarun ta, a kudancin ƙasar kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wutar ta yi tanadi.

Rukunin farko na sojoji, kimanin 6000 su girka sanssani a birnin Marjayoun da ke tazara kilomita 7 da iyakar Isra´ila.

Babban komandan rundunar sojojin Libanon, ya bayana cewar, nan da sa´o´i 24, sojojin za su bazuwa, a karbun iyakar da Majalisar Dinkin Dunia ta shata, tsakanin Isra´ila da Libanon.

Baki ɗaya, gwamnatin Beyruth, ta yanke shawara aika sojoji dubu 15, a yankin kudancin ƙasar.

Wannan shine karo na farko, tun bayan shekaru 40 da su ka gabata da sojojin ƙasar su ka sa ƙafa a yanki.

A nata ɓangare rundunar Isra´ila, ta miƙa fiye da rabi, na yankunan Libanon da ta mamaye, ga rundunar shiga tsakani ta Majalisar Dinkin Dunia.

A fagen diplomatia kuwa, ƙasashe da ƙungiyoyi daban-daban na ci gaba da mahaurori, a game da matakan aika rundunar sojojin, wada zata ƙara ƙarfi ga FINUL, da kuma tantance yaunin da ya rataya kan wannan runduna, kazalika, da kuɗaɗen da zata gudanar da a yuka.

A sati mai zuwa ne, a ke sa ran, Majalisar Dinkin Dunia, za ta fara aika gumen farko, na rundunar, inji Jannar Alain Pellegri, babban komandan dakarun Majalisar Dinkin Dunia a ƙasar Libanaon.

A dangane da batun, ministar harakokin wajen Isra´ila Zipi Livni, ta tantana da sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, inda ta bayanan cewar:

………………..

Ta ce: „ina kyautata zaton yanayi na gaskiya tantagarya ya bayyana a fagen diplomatia.

Aiki da ƙuduri mai lamba 1701 na tsagaita wuta, tsakanin Isara´ila da Hizbullahi, zai haifar da cenje cenje a yankin baki ɗaya, mussaman a Libanon, sannan mu duka zai haifar mana da mai ido, zuwa gaba“.

To saidai massana harakokin diplomatia, na nuna shaku a akan ɗorewa zaman lahia a wannan yanki, da ke yawan fama da riginginmu.

A game da haka, mataimakin sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia, Mark Malloch Brown cewa yayi:

„Yankin na cikin yanayi mai sarƙƙaƙiyar gaske, inda ko wa ma, na iya cinna wutar rikicin, da kan iya bazuwa dandannan.

A saboda haka, abu mafi a´ala ,shine cikin gaggawa, a samu kwance ɗamara yaƙi, sannan dakarun Libanon, da na Majalisar Ɗinkin Dunia, su kasance a yankin“.

A ɓangaren zirga zirga, kuwa, an buɗa filin saukar jiragen samar birnin Beyruth, bayan fiye da wata guda, da rundunar Isra´ila ta yi masa amen wuta.