1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta nada sabon shugaban MINUSCA

Lateefa Mustapha Ja'afarAugust 14, 2015

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nada sabon shugaban rundunar wanzar da zaman lafiya ta majalisar a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/1GFQD
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moonHoto: picture-alliance/dpa/I. Kovalenko

Sabon shugaban rundunar ta MINUSCA Parfait Onanga-Anyanga dan kasar Gabon ya maye gurbin tsohon shugabanta Babacar Gaye dan asalin kasar Senegal. Wanda majalisar ta kora bayan da aka zargi dakarun rundunar, da aikata miyagun laifuka da suka hadar da cin zarafin kananan yara ta hanyar yi musu fyade. Zargi na baya-bayan nan dai shine wanda kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta yi a makon da ya gabata wanda wata yarinya mai kimanin shekaru 12 ta shaidar da cewa daya daga cikin dakarun rundunar ta MINUSCA ya yi mata fyade yayin wani bincike da dakarun suka gudanar a gundumar PK5 da ke zama wajen da Musulmin kasar ke da zama. Kafin nadin Onanga-Anyanga a matsayin sabon jagoran rundunar ta MINUSCA a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai, shine jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar Burundi.