1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar shiga tsakani a kudancin Libanon

August 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bulj

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Dunia Kofi Annan da shugaba Georges Bush na Amurika, sun tantana ta wayar talho ,a yammacin jiya, a game da batun aika rundunar shiga tsakani ta Majalisar Dinkin Dunia a kudancin Libanaon.

Bush da Annan sun yi cimma matsaya daya a kann wajibcin tura wannan cikin gaggawa, ta la´akari da hadarinda ke tatre da tsagaita wutar da a ka cimma.

A daya hannun kuma magabatan 2 ,sun yi mansayar ra´ayoyi ,a game da rikicin makaman nukleyar kasar Iran da rikicin yankin Darfur na kasar Sudan.

Koffi Annan ya bada bayana halartar taron ministocin harakokinwaje na kungiyar gamayya turai ranar juma´amai zuwa a birnin Bruxelles wanda a sakamakon sa, ake sa ran EU zata gabatar da addadin tallafin ta,ga rundunar shiga tsakani a kudancin Libanaon.

Shima sahugaban darikar Roman katolika, Paparoma Benedikt na 16 ya jaddada kiora ga magabatan dunia da su ɗauki mattakan da su ka dace, domin samar da kwanciyar hankali mai ɗorewa, a yankin gabas ta tsakiya, ta ma dunia baki ɗaya.