1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar sojin Amurka ta kaddamar da hari a kudancin Somalia

January 9, 2007
https://p.dw.com/p/BuUz

Rundunar sojin Amurka ta kaddamar da hari ta jiragen saman yaki kan wadanda ta kira yan kungiyar Alqaeda da suka kai harin bam kan ofisoshin jakadancin Amurkan a kasashen Kenya da Tanzania a 1998.

Kafofin yada labarau na Amurka sun bada rahotonnnin cewa jirgin yakin Amurka kirarar AC 130 ya kai hari daga Djibouti zuwa kudancin Somalia bayan jamian leken asirin Amurka sun gano wadanda ake nema.

Rahotannin sunce daya daga cikin wadanda ake nema da laifin kai harin,wani shugaban al Qaeda a gabashin Afrika.