1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rushe ginin Otel na farko a tarihin Ghana

Isaac Kaledzi /Yusuf IbrahimApril 6, 2016

Ghana na daya daga cikin kasashe masu tarihi a Afirka ta Yamma. Saboda irin dangantakarta da turawan mulkin mallaka a lokacin da take neman yancin a 1950.

https://p.dw.com/p/1IQAt
Ghana Accra Demolished Sea view Hotel
Hoto: DW/Divine Agborli

A wancan lokaci dai kasar Ghana tana samun masu zuwa yawon shakatawa a ko wacce shekara, kuma sukan je kasar ne domin ganin ababen tarihi da kasar ke da su.

Wani gari mai suna James town da ke a babban birnin Accra na da gidajen tarihi masu yawa. Sea view Hotel shi ne Otel na farko a kasar ta Ghana wanda sarauniyar Ingila Elizabeth II ke sauka a duk lokacinta na yawon shakatawa da ganin kayan tarihi a shekara ta 1961. Kuma shi ne hotel mafi tsufa a kasar, kamar yadda Ussher Fort mazaunin garin ya bayyana.

"Wannan na daya daga cikin ababen tarihi da ke garemu a wannana garin kuma munada wani gida mai matukar tarihi gami da kuma wani gidan kaso, kuma idan ka duba muna da hotel na farko a Acra wato CV Otel".

Fort ya kara da cewar ana samun masu zuwa yawon shakatawa sossai saboda wannan Otel mai matukar tarihi. Sai dai ya bayyana wani akasi da aka samu game da otel din:

"CV Otel da sarauniya Elizebeth taima lakabi amma abIn mamaki kwana kwananan mai wurin ya zo yasa aka rushe wurin ya saida wa wasu mutane suka gina coci"

Mazauna wannan wuri sun yi matukar bakin cikin wannan mataki kamar yadda Clinton Ofori nunar:

"Ni tausayi ne ya kamani saboda wannan shi ne otel na farko a kasar Ghana amma sai dai kash an rushe wannan gini na yi matukar razana".

Gine-gine gami da kayayyakin tarihi na taka rawa a kasashe wajen samar masu da kudaden shiga wanda rusa gidajen tarihin ka iya kawowa kasa nakasu musamma ta hanyar samun kudin shiga.