1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Russia tayi alkawarin inganta samar da hayakin gas ga kasashen turai

January 3, 2006
https://p.dw.com/p/BvDy

A yau talata ne kamfanin samar da hayakin gas na kasar Russia yace zai inganta harkokin samar da hayakin gas din ga wasu kasashe na nahiyar turai, bayan da kwana biyu da suka gabata aka samu yan matsaloli.

Da yawa dai daga cikin kasashen dake sayen hayakin gas din sun soki lamirin kasar ta Russia da katse samar musu da hayakin gas din na wani dan lokaci.

Bisa hakan kuwa mahukuntan na Russia sun zargi kasar Ukraine ne da satar hayakin gas din da aka aikewa wasu kasashen na turai ta bututun man daya bi ta cikin kasar ta Ukraine.

Tuni dai kasar ta Ukraine ta karyata wannan zargi da cewa ba mai yiwuwa bane.

Rikici a tsakanin kasar ta Russia da Ukraine ya samo asali ne bayan da mahukuntan na Ukraine suka yi watsi da matakin karin farashi da kasar Russia tace zata yi a game da hayakin gas din da suke sayar musu.

Tuni dai kungiyyar gamayyar turai, wato Eu ta bukaci wadannan kasashe biyu dasu koma teburin shawara don warware wannan takaddama cikin ruwan sanyi.