1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwan sama mai yawa na kara kawo ciƙas ga aikin taimako a Afirka

September 24, 2007
https://p.dw.com/p/BuAR
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake kara zubawa musamman a gabashin nahiyar Afirka na kara tsananta mawuyacin hali da aka shiga a kasashe dake fama da ambaliyar ruwa. Ministan da ke kula da ayyukan taimakon jin kai na kasar Uganda Musa Ecweru ya ce ruwa ya malale kusan dukkan hanyoyin mota a yankunan da bala´in ya shafa. Hakan na kawo babban cikas ga masu aikin taimako. Tun a cikin yuli ruwan sama mai yawa da ake samu ya yi haddasa mummunar ambaliya a kasashe 18 na Afirka. sama da mutane 300 suka rasu yayin da dubun dubata suka asarar gidajensu sakamakon wannan ambaliya. Masu hasashen yanayi sun ce za´a kara samun wani ruwan sama mai yawa a wadannan kasashe.