Ruwanda ta bar sojojinta a Sudan
September 25, 2010Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasar Ruwanda ta yanke shawarar barin dakarunta masu lura da aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Sudan.Tun can da farko dai hukumomin na kasar sun yi barazanar janye sojojin nasu .
Rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana ya zargi sojojin kasar ta Ruwanda da aikata kisan kiýasu a gabacin jamhuriyar Kongo. Kasar ta Ruwanda dai na da dakaru kusan 3500 da ke can jibge a Sudan, wacce ke fuskantar barazana barkewar wasu sabbin tashe-tashen hankula, dangane da zaben rabar-gardama da ake shirin gudanar wanda zai baiwa yankin kudancin kasar 'yancin cin kashin kai .
A halin da ake ciki dai hukumomin na Khartum sun ce a shirye suke su amince da duk yadda sakamakon zaben ya kaya .
Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abbas