1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri'ar raba gardama Rwanda

Yusuf BalaDecember 18, 2015

Tuni dai wannan bukata ta neman tazarcen ta samu rashin goyon baya daga mahukuntan birnin Washington da Brussel.

https://p.dw.com/p/1HQ4u
Rwanda Referendum
Jami'ar zabe a wurin kada kuri'a a RwandaHoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Al'umma sun hau dogwayen layuka tun daga misalan karfe bakwai a ranar Juma'an nan a kuri'ar raba gardama da za ta ba wa shugaba Paul Kagame dama ta yin tazarce har zuwa shekarar 2034, yayin da mafi akasari al'umma ake sa ran za su yi na'am da shirin na tazarce.

Tuni dai wannan bukata ta neman tazarcen ta samu rashin goyon baya daga mahukuntan birnin Washington da Brussel wadanda suka bayyana shirin da cewa yin karantsaye ne ga dimokradiya a kasar da ke a Tsakiyar Afirka.

Da yake kada tasa kuri'ar shugaba Kagame ya ce abin da ke faruwa a kasarsa abu ne da al'ummar kasar ke bukata.

Masu kada kuri'ar dai cikin murana da kide-kide da raye-raye sun rika jefa kuri'arsu. Pasikaziya Ndakizera ta fitone daga yankin Kigali ta yi bayani kamar haka.

"Na kasance cikin farin ciki da wannan kuri'ar raba gardama saboda a yanzu mun samu tsaro a kasa, muddin shugabanmu na raye ba zamu samu rashin tsaro ba dan haka na zabi ya yi tazarce dari bisa dari".