1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sa ƙafar wando guda da 'yan zanga-zanga a Thailand

April 5, 2010

Matakin gwamnatin Thailand na murƙushe 'yan zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/Mni2
Framinstan Thailand, Abhisit Vejjajiva.Hoto: picture alliance / dpa

Shugabannin gwamnantin Thailand sun ce suna jiran kotu ta ba su ikon kore dubban jama'a da ke zanga-zangar nuna adawa da su, da suka yi wa cibiyar yawon buɗe da ke birnin Bangkok cincinrinzo. 'Yan zanga-zangar masu saye da jajaye riguna suna nuna goyon bayansu ne ga tsohon shugaban kasar, Thaksin Shinawatra, da aka tuntsurar a a shekara ta 2006. Zangar-zangar da suke gudanarwa tun makonni huɗu da suka gabata dai ta janyo durkushewar babban birnin ƙasar da ke zaman babbar cibiyar kasuwanci. Sai da ma suka yi wa ginin hukumar zaɓen ƙasar kawanya . Amma sai suka janye bayan da aka ba su tabbacin cewa hukumar tana gudanar da bincike game da zargin ba da tallafin kuɗi ga jam'iyyar Framinista Abhisit Vejjajiva, da ke mulki.

Mawallafiya: Halima Abbas

Edita: Umaru Aliyu

T