1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sa yara aikin ƙarfi na ƙaruwa a Afirka

May 10, 2010

ƙungiyar ƙodago ta duniya ta nuna damuwa game da bautar da yara ƙanana a Afirka.

https://p.dw.com/p/NKl1
Hoto: AP

ƙungiyar ƙodago ta duniya ta nuna damuwarta game da yaɗuwar da bautar da yara ƙanana ke ci gaba da yi a nahiyar Afirka. A cikin wani rahoto da ta wallafa a birnin Hague, ƙungiyar ta ce yaran da aka sa ayyukan da suka fi ƙarfinsu na ci gaba da ƙaruwa a wannan nahiya tamu. Rahoton ya ce kashi 60 daga cikin 100 na yaran da ta gano  ana bautar da su, 'yan asalin Afirka ne.

Manoma da kuma masinta na daga cikin waɗanda suka fi ƙaurin suna wajen sa yaran da ke da ƙasa da shekaru 14 da haihuwa aikin da ya fi ƙarfinsu a ƙasashen na Afirka. ƙungiyar ta ƙodago ta duniya ta kuma bayyana cewa ba a damuwa da karantunsu da kuma kiwo lafiyansu a wuraren da ake bautar da sun. 

Wasu alƙalamun Majalisar Dinkin Duniya sun nunar da cewa ta fitar da sanarwa cewar ana azabtar da yara kanana da yawansu ya kai miliyan 245.5, kana miliyan 115 na aikin dake kawo cikas ga lafiyar jikinsu. 

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar