1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saban Praministan riƙwan ƙwarya a Cote d´Ivoire

Yahouza S.MadobiApril 5, 2007

Charles Konnan Bany ya miƙa mulki ga Guillaume Sorro

https://p.dw.com/p/Btvr

A yammacin jiya ne, a birnin Abidjan na ƙasar Cote d´Ivoire, a ka yi bikin miƙa mulki daga hannun Praminista riƙwan ƙwarya Charles Konnan Banny, zuwa ga wani Pramistan riƙwan ƙwaryar Guillame Soro, magudun yan tawayen FN.

Jim kaɗan kamin bikin saida Charles Konnan Bany yayi bankwana da minsitocin sa, tare da yin bitar mahimman ayyukan da ya gudanar a zamanin sa wato,daga watan desember na shekara ta 2005 zuwa yanzu.

A jimilce, wannan ayyuka sun jiɓanci batun samar da zaman lahia a ƙasar Cote d´Ivoire, da ta faɗa rikicin tawaye a tsawan shekaru fiye da 4.

Charles Konnan Bany, ya gabatarwa Guillaume Sorro babban ƙalubalen da ke jiran shi:

Aikin farko ya shafi rijistan masu zaɓe a faɗin ƙasa baki ɗaya, sai kwance makamai, ga dakarun tawaye, da na sa kai, masu goyan bayan shugaban ƙasa, sannan tabbatar da haɗe Cote d´Ivoire, ƙasar da ke rabe gida 2, tun, shekarara ta 2002.

Saban Praministan ya yi yabo da jinjina damtse ga magajin sa, wanda acewar sa ya taka mahimiyar rawa, ta fanin samar da zaman lahia aCote d´Ivoire.

A ɗaya hannun Guillaume Sorro ya gabatar da jawabi, inda ya alkawarta yin aiki bil haki da gaskiya domin shafe hawayen al´ummomin ƙasar Cote D´Ivoire, a game da matsalolin tsaro da na taɓarɓarewar tattalin arziki.

Guillaume Sorro ya bukaci tsofan Praministan ya ci gaba da kasancewa tare da shi domin ba shi shawarwari na cimma burin da aka sa gaba.

Ɓangarorin gwamnatin Cote d`ivoire da na yan tawayen FN, sun cimma yarjejeniyar shinfiɗa zaman lahia a ƙasar a sakamakon taron birnin Ouagadougou na ƙasar Burkina Faso, bisa jagorancin shugaba Blaise Campaore, wanda Lauran Bagbo, ke nuni da kanwa uwar gami, ta hanyar taimaka wa yan tawaye.

Kamin nan da 8 ga watan da mu ke ciki a ke sa ran, saban Praminista Guillaume Sorro, zai gabatar da sabuwar gwamnatin, wadda zata ƙunshi ministoci 33.

Shugaban ƙasa zai bada ministoci 15 a yayin da ɓangaren tawaye zai kawo 18