1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saban shugaban ƙasar Benin Yayi Bonny yayi jawabin farko ga jama´a

March 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv42

Saban shugaban ƙasar Benin, Thomas Yayi Bony, da a ka zaba ranar lahadi ta wuce, yayi jawabin farko, tun bayan bayyana sakamakon zaɓen.

A jawabin na sa,ya yi mattukar godiya, ga al´umar Benin da ta ɗora masa wannan yauni, ya kuma yi alkawarin yin aiki tukuru, domin maida alheri ga al´ummar ƙasa.

YA ce, tunni ya ɗaura damara, domin shiga yaƙi gadan gadan, na haɓɓaka tatalin arzikin Benin da kauttata rayuwar jama´ar wannan ƙasa, da ke fama da matsaloli daban-daban.

Ranar 6 ga watan Aprul mai zuwa, Yayi Bonny,zai gaji Mathieu Kereku, shugaba mai barin gado, wanda kuma, yayi mulkin Jamhuriya Benin,a tsawan shekaru 28.

Masu kulla da harakokin siyasa a ƙasar na ɗaukar saban shugaban, a matsayin wanda ke da kaffar samar da ci gaba, ta la´akari da muƙƙaman da ya riƙe ta fanning tattalin arziki.

Bony ,ya rike matsayin gwaman babban bankin ƙasashen Afrika ta yamma, kazalika, ya laƙanci ƙabli da ba´adin harakokin tattalin arzikin ƙasa da ƙasa, sannan ga shi da sanayya da kafofin kuƙi na dunia.