1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saban yunƙurin cimma zaman lahia a Darfur

April 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuNd

Nan gaba a yau ne jami´an diplomatia na Majalisar Dinkin Dunia,da na tarayya Afrika, za su fara zaman taro a birnin New York na Amurika, a game da rikicin yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Saidai tunni, kamin fara taron, ministan harakokin wajen Sudan Lam Khol, ya jaddada matsayin gwamnatin Khartum, na ƙin amincewa da karɓar dakarun shiga tsakani na Majalisar Dinkin Dunia a Darfur.

Saidai a cewar sa, Sudan ta amince a ƙara yawan sojojin ƙungiyar tarayya Afrika.

Wasu rahottani da kafofin sadarwa na Saudi Arabia sun ruwaito cewar, shugaba El Bashir na Sudan, ya tantana ta wayar talho, tare da Sarki Abdalah, inda ya bayyana amincewa da kara sojojin na AU.

Masharanta na hasashen cewar, tantanawar ta yau, ba zata haifar da wani abun azo a gani ba,saidai kawai Sudan ta maimata matsayin da aka riga aka sani, wato, amincewa da karaɓar dakarun shiga tsakani, na Majalisar Dinkin Dunia,amma ba tare da jirage masu saukar angulu ba.