1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani a Jamus kan 'yan gudun hijira

Mouhamadou Awal BalarabeOctober 10, 2015

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da gwamna jihar Baveriya Horst Seehofer na ci gaba da samu rashin fahimta kan batun kwararar 'yan gudun hijira na Syriya.

https://p.dw.com/p/1Gm21
Archivbild Angela Merkel und Horst Seehofer
Hoto: Imago

Gwamnan Jihar Baveriya da ke Kudancin Jamus Horst Seehofer ya yi barazanar kai gwamnatin tarayya kara a gaban kotun tsarin mulki, a kan shirinta na bude kofofin kasar ga dubban 'yan gudun hijiran Syriya. A lokacin da yake tsokaci a kan wannan batu ga manaima labarai, Seehofer ya ce zai dauki matakan da suka dace don dakile kwararar 'yan gudun hijiran ta hanyar rufe iyakokin jihar tasa ta Baveriya.

Sai dai kuma a lokacin da ya ke mayar da martani ministan da ke kula da al'amuran cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere, ya ce barazanar ba ta kan gado, saboda rufe kan iyakar Jamus da Austriya ba zai iya dakile kwararar 'yan gudun hijira ba.

Wannan na zuwa ne dai a daidai lokacin da 'yan gudun hijiran ke ci gaba da fuskantar hare-hare a nan Jamus, inda alkaluma suka nunar da cewar adadin hare-haren ya kai 500. Lamarin da ya ninka idan aka kwantanta da hare-haren da masu neman mafaka suka fuskanta a Jamus a shekara ta 2014.