1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani a ma'aikatar harkokin wajen Jamus

March 30, 2005

Kimanin jami'an diplomasiyya 70 suka rattaba hannu kan wata takarda ta adawa da salon kamun ludayin ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer

https://p.dw.com/p/Bvce
Schröder da Fischer da Schily a tabargazar nan ta visa
Schröder da Fischer da Schily a tabargazar nan ta visaHoto: AP

A ‚yan kwanakin baya-bayan nan korafi a game da sakon ta’aziyyar dangane da jami’an diplomasiyyar Jamus da suka rasa rayukansu ya kara tsananta. Rahotanni masu nasaba da kafofin yada labarai sun ce kimanin jami’an ma’aikatar harkokin waje su 70 suka rattaba hannu akan wata takardar dake neman kakkabe ministan harkokin waje Joschka Fischer daga bakin aikinsa. Ministan harkokin wajen na Jamus dai ya tsayar da shawara ne cewar ba zai taba gabatar da ta’aziyya a mujallar ma’aikatarsa ga jami’an diplomasiyyar da suka taba wanzuwa karkashin tutar NSDAP ta ‚yan nazi ba. Duka-duka abin da za a rika yi shi ne ba da sanarwar rasuwar kawai, ba tare da wata kalma ta ban girma ba. Wannan kuwa gyara ne ministan yayi dangane da matakin da ya dauka tun farko a shekara ta 2003 na cewar hatta sanarwar mutuwarsu ba abu ne da ya kamata a shigar da shi a mujallar ma’aikatar harkokin waje ba. Su dai masu korafi a game da shawarar ta Fischer suna tattare ne da ra’ayin cewar bai kamata a yi watsi da irin gagarumar gudummawar da wani jami’in diplomasiyya da bayar bayan yakin duniya na biyu ba. Kuma ko da yake akwai masu goyan bayan ra’ayin ministan harkokin wajen, amma kasancewar sama da jami’ai 70 suka rattaba hannu kan takardar ta adawa, abu ne dake bayani dalla-dalla akan rashin gamsuwar dake tattare a zukatan jami’an ma’aikatar harkokin wajen Jamus yanzu haka. Wannan ci gaba kuwa ya fara ne sannu a hankali sannan tabargazar nan ta ba da visa a ofososhin jakadancin Jamus na gabacin Turai, da ake dora alhakinta akan ministan harkokin waje Joschka Fischer ta kara rura wutar rikicin. Da yawa daga jami’an diplomasiyyar na tattare da ra’ayin cewar tun da dadewa magabata a ma‘aikatar harkokin wajen ke da masaniya a game da wannan tabargaza, amma sai suka yi mata rikon sakainar kashi, lamarin da ya kai ga zargin jami’an diplomasiyyar Jamus da mara wa miyagun mutane baya da kuma bata sunan kasarsu. An saurara daga wani tsofon jami’in diplomasiyyar Jamus yana mai bayanin cewar wannan tabargaza da sanya tababa a game da manufofin ketare na kasar ta kuma taimaka wajen zubar da martabar ma’aikatar harkokin wajen a idanun jama’a a sassa daban-daban na duniya. Wani abin da ya kara ba ta wa mutane rai ma shi ne yadda shi kansa ministan da farkon fari yake batu a game da wasu 'yan kurakurai kafin daga baya ya dauki matsalar da muhimmanci. A halin yanzu haka ‚yan hamayya na neman yin amfani da wannan dama domin ganin lalle Fischer ya ba da shaida a gaban kwamitin rikon kwarya na majalisar dokoki dake bin bahasin lamarin tun kafin zaben majalisar jihar Northrhine-Westfaliya da za a gudanar ranar 22 ga watan mayu mai zuwa.