1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani tsakanin kungiyoyin kwadago kan yajin aiki

Kamaluddeen SaniMay 18, 2016

Kungiyar kwadagon Najeriya ta sake daukar alwashin tsunduma yajin aikin duk kuwa da umarnin da kotun ma'aikatan kasar ta bayar kan dakatar da kungiyar.

https://p.dw.com/p/1IpcN
1. Mai-Kundgebung in Abuja
Hoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Ana dai sa ran kungiyar zata fara yajin aikin ne a ranar Larabar nan domin tilastawa gwamnatin Najeriya dawo da farashin man na da wato naira 86.50 mai makon naira 145 da yanzu haka gwamnatin ta kara.

Shugaban hukumar kwagadon Ayuba Wabba a yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja ya bayyana cewar har yanzu sun kasa samun matsaya da gwamnatin a don haka basu da wani zabi illa iyaka su fara yajin aikin.

To sai dai a hannu guda, shugaban hadaddiyar kungiyar TUC Bobboi Kaigama a nasu bangaren sun dakatar da shiga yajin aikin kuma sun akira ga mabobin 'ya'yan kungiyar da cigaba da gudanar da harkokin su kamar yadda aka saba.

Gwamnatin Najeriya dai ta nanata cewar ta dauki wannan matakin ne sabili da karancin mai gami da faduwar farashin sa a kasuwar mai ta Duniya.