1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

010809 Bundeswehr Afghanistan Richtlinien

August 3, 2009

An gabatar da sabbin ƙa´idoji da suka shafi aikin sojojin Jamus a arewacin Afganistan

https://p.dw.com/p/J2xd
Ministan tsaron Jamus Franz Josef JungHoto: AP

Rundunar sojin Jamus na ƙara fuskantar hare-hare a arewacin Afghanistan. Duk da cewa har yanzu ministan tsaron ƙasar ta Jamus Franz Josef Jung na ƙin yin magana game da wani yaƙi da sojojin ke yi, amma an sake yin kwaskwarima ga ƙa´idojin amfani da makamai ga sojojin. Sabbin ƙa´idojin sun sauƙaƙa damar amfani da makaman ba da wani ɓata lokaci ba.

Masu adawa da aikin rundunar sojin ta Jamus sun bayyana wannan kwaskwarima da ainihin halin yaƙin da ake ciki a Afghanistan yayin da masu goyon baya kuma ke magana dangane muhimmancinsa kuma zai bawa sojojin ƙarin damar tafiyar da aikinsu. Kawo yanzu sojojin na amfani da makamai ne idan hakan ya zama tilas wato idan suna cikin barazana ko kaiwa abokan aikinsu ɗauki. Kuma dole sai sun yi gargaɗi kafin su harba makami musamman saboda kasancewar aikin dakarun ƙasa da ƙasa a Afghanistan na samar da zaman lafiya ne amma ba yaƙi ba. To amma sabbin dokokin da ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung ya amince da su ba a fayyace su dalla-dalla ga jama´a ba. To amma rahotanni sun dace cewa dokokin sun ba da izinin harbe abokin gaba dake tserewa idan akwai fargabar cewa yana iya sake kai hari. Thomas Sohst shi ne shugaban reshen ƙungiyar rundunar Jamus ta Bundeswehr a yammacin ƙasar ya ce sabbin ƙa´idojin sun dace.

"Muhimmancinsa shi ne aikin soji ya haɗa da fatattakar abokan gaba. Saboda haka muhimmin abu ne idan suka samu izinin tafiyar da waɗannan ayyukan gaba ɗaya. Dole ne a yi aiki da doka idan da akwai wasu hanyoyin da suka ba da damar murƙushe abokin gaba, za mu yi yanke shawara da takwarorinmu na Afghanistan kafin a yi amfani da bindiga akan wani."

Dalilin yiwa ƙa´idojin kwaskwarima shi ne sabon yanayin yaƙi da aka shiga a arewacin Afghanistan. A shekarun baya mayaƙan Taliban sun taƙaita hare haren da suke kaiwa sansanonin rundunar ta Bundeswehr dake Kundus a cikin dare amma tun ´yan watanin baya-bayan nan sojojin na Jamus na yawaita samun kansu cikin musayar wuta da ´yan Taliban, musamman a wannan lokaci da ake shirye shiryen gudanar da zaɓen shugaban ƙasar a ranar 20 ga watannan na Agusta faɗan ya ƙara ƙazanta. Sojojin Jamus ɗin dai suke ƙoƙarin tabbatar da tsaro a yankunan dake kewayen Kundus inda ´yan tawayen ke da ƙarfi, inji shugaban ƙungiyar rundunar Bundeswehr Kanal Ulrich Kirsch.

"Abokan gabarmu a Afghanistan na sauya dubarun yaƙinsu. Suna ƙara ƙwarewa tare da horas da sabbin mayaƙa. Suna dagewa ga duk wata fafatawa ta lokaci mai tsawo. Wannan wani sabon salo ne na yaƙi."

Don ganin sojojin kiyaye zaman lafiya sun gane sabbin ƙa´idojin a filin daga yanzu haka an taƙaita bayanan a cikin wani ɗan ƙaramin littafi da za su iya sakawa aljihu.

Masu adawa da sabbin ƙa´idojin na ƙorafin cewa idan aka faɗaɗa aikin sojojin to tamkar an ƙara yawan barazanar da suke fuskanta ne musamman na yin fito na fito da ´yan tawaye. To amma rundunar Bundeswehr na mai ra´ayin cewa an bawa sojojin horo da ya dace ta yadda za su iya tinkarar ko wane hali da za su samu kansu a ciki.

Mawallafa: Daniel Scheschkewitz/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala