1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

140410 Blogger Pressefreiheit

April 15, 2010

Hanyar sadarwa ta intanet na bawa 'yan adawa a ƙasashen da ake tafiyar da mulkin kama karya, wata sabuwar dama ta musaya da kuma yaɗa labarai, inda suke biris da matakan gwamnati na tace labarai

https://p.dw.com/p/Mwxe
Facebook na daga cikin sabbin dandalin musayar ra'ayoyi a intanet

Akan haka a birnin Berlin na nan Jamus, a ranar Laraba aka buɗe wani babban taron kwanaki uku da aka yiwa laƙabi da Republica. Wannan taro dake duba muhimmancin da intanet ke ƙara samu a matsayin wata kafar yaɗa labaru da musayar bayanai, yana da muhimmanci musamman ga masu amfani da intanet ɗin.

Duk ƙoƙarin da za a yi na toshe kafar samun bayanai ta intanet ba zai yi nasara ba. Domin a kullum masu amfani da intanet ɗin na da hanyoyi daban daban na samun labarai. Alal misali a cikin watan Maris lokacin da kamfanin taimakawa neman bayanai ta intanet wato Google ya rufe na'urarsa a China don nuna fushinsa ga manufofin hukumomin ƙasar na tursasawa masu amfani da intanet, masu amfani da yanar gizon sun gano sabuwar hanyar samun bayanai daga yankin Hongkong. Michael Anti masani ne kan harkar yaɗa labarai ta intanet.

Ya ce: "Wani lokaci idan kana neman bayani ta Google sai ka ga hanya ta katse. Daga nan za ka gane an toshe ta ne. Saboda haka yanzu mutane da yawa sun gane hakan, shi yasa sai su nemi sabuwar hanyar kaucewa hanyar da aka toshen zuwa wadda za su iya shiga kai tsaye."

Su ma 'yan Iran sun shaida haka, inda a zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a bara, masu amfani da sabuwar kafar intanet da ake kira Blog suka nuna basirarsu wajen watsa labarai saboda rashin samun shiga kafofin yaɗa labaru na hukuma, kamar yadda Farnaz Seifi ' yar Iran mai amfani da hanyar Blog ta nunar.

Ta ce: "Watanni biyu gabanin zaɓen ba a ga wani yanayi na yaƙin neman zaɓe ba. Mutane ba su san komai game da Mir Hussein Mussawi ba ɗan takarar masu neman sauyi. Masu amfani da kafar Facebook da Blog suka fito da shi fili har kampen ɗin ya yi armashi."

Duk da cewa Mussawi ya sha kaye amma shakkun da aka nuna dangane da sahihancin sakamakon zaɓen ya ta da zanga-zanga inda aka yi amfani da sabbin hanyoyin sadarwa na Facebook da Twitter. Duk ƙoƙarin da hukumomin Iran suka yi na toshe waɗannan hanyoyin ba cimma nasara ba, domin an ci-gaba da yaɗa hotuna da labarai dangane da zanga-zangar adawa da gwamnati.

A ƙasar Rasha ma inda gwamnati ke tace labaru a telebijin, mutane na ƙara karkata ga amfani da intanet. Wani masanin kafar sadarwa ta Blog a Rasha Rusten Adagamow ya ce har yanzu ƙasar ba ta tace labaru ta intanet a saboda haka masu adawa da ita na da sauƙin samun bayanai a kafar Blog.

Ya ce: "Wannan shi ne ɗaya daga cikin batutu masu wahala, domin ana tsokana sannan ana amfani da wasu labaran don cimma wata manufa. Saboda haka dole sai ka yi takatsatsan. Mun fi dogaro ga waɗanda muka amince da su."

Gwagwarmayar saka labarai a intanet bata tsaya a ɓangaren fasaha kaɗai ba. A China alal misali gwamnati na ba da tukuici ga wanda ya rubuta sharhi dake bayyana ra'ayinta kuma ya buga a intanet. To amma ga 'yan adawa wannan ba matsala ba ce domin ba mai yarda da gaskiyar sa.

A daren yau DW za ta ba da lambar yabo ta kafar sadarwar intanet ta Blog a birnin Berlin sannan a rufe zauren taron a Juma´ar nan.

Mawallafi: Matthias Bölingen/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu