1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin hanyoyin tallafa wa aiyukan raya kasa

Yusuf BalaJuly 16, 2015

Taron kolin neman hanyoyin daukar nauyin aiyukan raya kasashen masu tasowa ya zayyana wasu dabaru da nufin samar da ci gaba mai dorewa.

https://p.dw.com/p/1G0F7
Äthiopien International Conference on Financing for Development in Addis Abeba
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Wondimu Hailu

Kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya sun cimma matsaya kan sabbin hanyoyin da za a bi wajen daukar nauyin aiyukan raya kasa. Wannan dai na zuwa ne bayan kwashe kwanaki uku ana tafka muhawara a taron da aka yi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha kan bukatar kudade da za a yi amfani da su a aiyukan ci gaba bayan shekarar 2015.

Taron kolin har wayau ya zayyana wasu hanyoyi ko dabaru sama da dari da za a iya amfani da su dan samun cimma burin samar da ci gaba mai dorewa a tsakanin kasashen. Sai dai kasashe masu tasowa sun gaza cimma buri wajen ganin an kafa wata cibiya da za ta rika lura da harkokin da suka shafi tattara haraji a duniya.

Nasara ga dukkan kasashen duniya

Mista WU Hongbo, da ke jagorantar fannin tattalin arziki da zamantakewa a Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana taron da cewa baki dayansa nasara ce ga kasashen masu tasowa da wadanda suka ci gaba.

"Ajandar taron na birnin Addis Ababa ta fitar da wani ginshiki mai kwari da zai taimaka wajen aiwatar da ci gaba mai dorewa wanda za a fara amfani da shi a watan Satumba a birnin New York, karkashin abubuwan da aka cimma. Za a duba yadda kudade ke shigowa a kasashen, sannan a ga yadda ake wasu tsare-tsare da za su tallafa a fannoni na zamantakewa da tattalin arziki da muhalli wadanda su ne za a ba wa fifiko."

Äthiopien International Conference on Financing for Development in Addis Abeba
Ban Ki-moon yana gaisawa da Shugaban Senegal Macky Sall a zauren taron na Addis AbabaHoto: Reuters/T. Negeri

Karkashin shirin ita ma kungiyar Tarayyar Turai ta yi alkawarin tallafa wa kasashe da ke a baya wajen bunkasar tattalin arziki kamar yadda Mista Hongbo ke cewa.

"Da shirin kungiyar Tarayyar Turai na tallafa wa kasashe da ke zama koma baya wajen ci gaban tattalin arziki inda za ta basu kashi 0.2 cikin 100 na abinda kasashensu ke samu a shekara nan da shekarar 2030. Sun kuma amince cewa za su kara harkokin zuba jarinsu a kasashen hadi da tallafi na kudi da gudunmawar kwararru."

Rashin kasuwanci da bibiyar kudaden haraji

A dai kasashen masu tasowa musamman a nahiyar Afirka rashin kasuwanci da ke tafiya da sanya idanun hukuma dan samun kudaden haraji abu ne da ke kawo musu cikas kamar yadda Mista Degol Mendes sakataren tsare-tsare a kasar Guinea Bissau ke cewa.

Äthiopien International Conference on Financing for Development in Addis Abeba
Shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim lokacin jawabinsa a taron na Addis AbabaHoto: picture alliance/AA/M. Wondimu Hail

"Guinea Bissau kasata, kasa ce da ke da fannin kasuwanci wanda ba ya karkashin tsarin hukuma, abun da ke haddasa karancin samun kudaden shiga masu yawa a fannin haraji. Kuma burin shi ne a samar da hanyoyin samun shigar kudade masu yawa, ta yadda za a samu janyo hankulan 'yan kasuwa masu zuba jari. Baya ma ga kasa irin Guinea Bissau, wasu kasashe su ma suna da nasu tsari wanda suke son ta hanyarsa su cimma burin bunkasa tattalin arziki. Ta sabili da haka ne ma muka hadu a nan domin nazarin samun kudaden aiwatar da wadannan aiyuka don nan gaba a samu wata duniya mai hadin kai da babu talauci."

Kungiyoyin fafutika dai sun cika da burin ganin a taron na Addis Ababa an samar da wata cibiya da za ta sanya idanu kan kasashe da ba sa biyan haraji yadda ya kamata, musamman manyan kasashe da ke harkoki da kanana masu tasowa dan tilasta musu. Sai dai kawai taron ya kare da kiran kwamitin masana a harkokin kasa da kasa kuma kwararru kan harkar haraji a Majalisar Dinkin Duniya su kara karfin aikinsu.