1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin manufofin Amurka a Iraki

January 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuVO

Shugabannin jamiiyar Democrats dake Amurka ,sunyi kira ga shugaba George W Bush da kada ya kara yawan dakarun kasar zuwa Iraki,kwanaki kalilan gabannin gabatar da sanarwarsa kann wannan yunkuri.Gwamnatin shugaba Bush dai ta tabbatar dacewa,zata maye guraben manayan jamian dakarun Amurkan dake Iraki,a bangaren wannan sabon manufa nata a a wannan kasa.Wasu daga cikin sauye sauye da aka sanar sun hadar da nadin Directan hukumar asirin kasar John Negroponte zuwa matsayin mataimakin sakatariyar harkokin waje,da mayar Navy Vice Admiral Michael McConnell mai ritaya,wajen mukamin Negroponte.To sai dai wadannan mukamai zasu tabbatu ne kadai bayan amincewan yan majalisar Dottijai na Amurkan.