1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin matakan yaki da masu tayar da kayar baya a Najeriya

Zainab Rabo RinginDecember 11, 2015

Rundunar sojojin Najeriya wadda ta duba mahimman kalubalen da ke a gabanta, ta sha alwashin daukan matakai a cikin wata sanarwa da ta fitar a karshen zaman taronta.

https://p.dw.com/p/1HLuf
Hoto: DW

Daraktan tsare-tsare na rundunar sojojin na Najeriyar ne manjo janar Jack Ogunaye ne ya karanta sanarwar bayan taro mai dauke da kudurori tara. Cikin sanarwar sojojin Najeriyar sun bayyana aniyarsu ta sanya tsofaffin sojojin kasar da suka yi ritaya cikin yakin da suke da kungiyar Boko Haram, sojojin sun kuma nuna damuwarsu kan yunkurin tada zaune tsaye da wasu tsageru ke yi a yankin Gabashin Najeriyar da sunan kafa kasar Biafra, inda suka ce za su dauki mataki a kansu. A hannu guda kuma sojojin sun bayyana matsalar harshe tsakaninsu da takwarorinsu na kasashe renon Faransa a matsayin babban kalubalen da ke kawo cikas a yaki da Boko Haram din, inda suka yanke shawarar bawa sojijin darasin harshen Faransanci a nan gaba.