1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin ministoci a Najeriya

August 10, 2010

Shugaban Najeriya zai yiwa majalisar gwamnatinsa garan bawul, inda zai shigar da 'yan adawa.

https://p.dw.com/p/OhwC
Jonathan Goodluck.Hoto: AP

Majalisar dattawan Najeriya ta amince da sabbin sunayen ministoci uku, waɗanda shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar musu. Biyu daga cikin waɗanda majalisar ta amince da sunayensu, sun fito ne daga yankin arewacin ƙasar wanda shugaba Jonathan yake zawarcin, don zarcewa da mulki, a dai-dai lokacin da ake ta cece kuce bisa tsayawarsa takara a baɗi. Wata majiya daga fadar gwamnati dake Abuja, tace za'a ƙara miƙa wasu sunayen minstocin, ƙasa da watanni shida kafin zaɓen shugaban ƙasas da gwamnoni dana 'yan majalisun ƙasar. Waɗanan sabbin ministocin sun haɗa da Salamatu Sulaiman tsohuwar ministar ma'aikatar mata, da kuma Yabawa Waɓi, dukkaninsu matane dake cikin jam'iyar ANPP, da suka fito daga jihohin Kebbi da Borno. Masu sharhi sukace koda cike dama a wacan majalisar ministocin marigayi 'Yar'aduwa akwai 'yan ANPP, amma wannan matakin an yi shi ne don rage ƙarfin da jam'iyar adawa mafi girma a ƙasar gabanin zaɓe.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu