1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin tashe tashen hankula a Iraki

January 29, 2006
https://p.dw.com/p/BvAS

A jiya asabar wani dan harin kunar bakin wake ya ta da bam da ya dana cikin wata mota inda ya halaka kansa da kuma sojojin Iraqi 4 dake sintiri a kusa da kauyen hambararren shugaban Iraqi Saddam Hussein. Harin wanda ya zo kwana guda kafin sake komawa ga zaman shari´ar da ake yiwa Saddam a yau lahadi, ya auku ne a kusa da kauyen Ojah mai nisan kilomita 180 arewa da birnin Bagadaza. Wasu sojoji 6 sun samu rauni a wannan hari. A kuma can birnin Iskandariya mutane 10 sun rigamu gidan gaskiya sannan 3 sun jikata a wani harin bam. ´Yan sanda sun ce an dana bam din ne a cikin wani kantin sayar da kayan zaki, dake wannan birni na ´yan Sunni. Wani sojin Amirka ya rasu a wani harin bam a birnin Bagadaza. Sannan ´yan sanda sun gano gawawwakin fararen hula 7 da aka yiwa kisan gilla a birnin Karbelah mai tsarki ga ´yan shi´a.