1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin tashe tashen hankula a Iraki

December 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvFD

`Yan Iraqi 18 ciki har da sojoji 2 da ´yan sanda 4 aka kashe a jerin hare hare da aka kai a fadin kasar a yau asabar. Majiyoyin tsaro sun ce an gano gawawwaki 8 a sassa daban daban na kasar. Wasu fararen hula 3 sun rasa rayukansu a wani harin gurnati da aka kai dazu dazun nan a tsakiyar birnin Samarra dake arewa da bagadaza, yayin da ´yan sanda 3 suka gamu da ajalinsu a wani hari da aka kan su a birnin Baquba arewa maso gabashin Bagadaza sannan dan sanda daaya ya rasa ransa a birnin Mosul. A kuma birnin Bagadaza fararen hula 3 aka kashe lokacin da wasu ´yan bindiga suka bude wuta akan motarsu. Tashe tashen hankulan dai su ne mafi muni tun bayan kammala zaben ´yan majalisar dokoki a ranar 15 ga wannan wata. A kuma halin da ake ciki ´yan shi´a sun yi watsi da kiran da ´yan sunni suka yi na a sake gudanar da wannan zabe, sakamakon magudin zabe da ´yan sunni suka ce an tabka.