1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin tashe tashen hankula a Iraki

October 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvOF
Mutane da dama sun mutu sakamakon wasu jerin hare-haren bama-bamai da aka kai a fadin kasar Iraqi. A birnin Tikrit dake arewacin kasar dan sanda daya da kuma kananan yara 4 sun rasu a fashewar wani bam a cikin wata babbar mota. Sannan a tsakiyar birnin Bagadaza mutane 4 suka rigamu gidan gaskiya sakamakon wani harin bam. A dangane da kuri´ar raba gardama akan kundin tsarin mulkin kuma har yanzu babu wani karin bayani akan sakamakon wannan kuri´a, baya ga na larduna 13 daga cikin 18 na kasar. A lardin ´yan sunni na Salaheddin ne kadai aka jefa kuri´ar yin fatali da sabon kundin tsarin mulkin.