1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon babin siyasa a Australia

Ibrahim SaniNovember 24, 2007
https://p.dw.com/p/CSdu

An fara kada kuri´ar zaɓen sabbin ´ Yan Majalisar dokoki a ƙasar Australia. Kuri´ar jin ra´ayin Jama´a ta baya- bayan nan na nuni da cewa Jam´iyyar Lebo ta Shugaba Kevin Rudd da alama ita za ta yi nasara kan Jam´iyyun haɗaka da Faraminista John Howard ke jagoranta. Kafafen yaɗa labarai sun rawaito Mr Rudd na alƙawarin janye sojin ƙasar dake Iraƙi tare da sa hannu kan yarjejeniyar Kyoto, bayan samun nasarar zaɓen na yau. Mr John Howard wanda ya shafe shekaru 11 ya na jagorancin ƙasar, ya ce idan ya samu nasarar yin tazarce a karo na biyar, to zai yi murabus shekaru biyu a cikin wa´adin tare da mika mulki ga ministan kuɗi na ƙasar Peter Costello.