1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bincike kan wani ɓangare na jirgin sama da aka samu

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 30, 2015

Mahukuntan ƙasar Faransa na yin nazari a kan wani ƙaton ɓangare na jirgin sama da aka gano a Tsibirin Reunion na tekun Indiya da ake kyautata zaton na jirgin Malesiya da ya yi ɓatan dabo ne.

https://p.dw.com/p/1G7F1
Bincike a kann bangaren jirgin saman da aka samu.
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Pitou

Jirgin saman samfurin Boeing 777 mai lamba Mh370 ya ɓace a watan Maris na shekarar da ta gabata ta 2014 ɗauke da mutane 239 da suka hadar da fasinjoji da ma'aikatan jirgin a wani haɗarin jirgin sama da aka bayyana da mafi tashin hankali a tarihi. Wani kwararre a kan kirar jiragen sama ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar ɓangaren jirgin da aka gano ɗin na jirage ne samfurin Boeing 777 makamancin na kamfanin jirgin sama na 'Malaysia Airlines' da ya ɓace, sai dai ya ce babu tabbacin cewa na wannan jirgin ne. Kwararrun masu bincike a kan musabbabin haɗarin jiragen sama na ƙasar Faransa da takwarorinsu na Ostareliya da kuma Malesiya na yin nazari a kan ɓangaren jirgin da aka gano a kusa da tsibirin ƙasar Faransa da ke Gabashin ƙasar Madagaska, sai dai sun ce ya yi wuri a tabbatar da cewa na jirgin Malesiyan da ya yi ɓatan dabo din ne.