1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawo karshen rikicin Ukraine

Lateefa Mustapha Ja'afarAugust 27, 2015

Bangarorin da ke yakar juna a kasar Ukraine sun ce za su dakatar da karya ka'idojin yarjejeniyar sulhun da suka cimma a tsakaninsu a birnin Minsk.

https://p.dw.com/p/1GMfc
Rikicin Ukraine da kokarin tsagaita wuta
Rikicin Ukraine da kokarin tsagaita wutaHoto: picture alliance/NurPhoto

Kungiyar tsaro da hadin kan Turai OSCE ce ta sanar da hakan, inda ta ce bangaren gwamnatin Ukraine din da kuma 'yan awaren gabashin kasar da ke goyon bayan Rasha sun amince su fara mutunta yarjejeniyar sulhun yadda ya kamata daga ranar daya ga watan Satumba mai zuwa, ranar da makarantun kasar za su fara zangon karatunsu na wannan shekara. Kawo yanzu dai akwai manyan makamai na duka bangarorin biyu a filin daga wadanda ba a janyesu ba, duk kuwa da cewa yarjejeniyar da suka cimma a birnin Minsk din a watan Fabarairun da ya gabata ta tanadi hakan.