1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon jadawali zaɓe a Nigeria

July 21, 2010

Watan janairu na shekara ta 2011 majalisar dattijan ta tsayar a gudanar da zaɓuɓukka.

https://p.dw.com/p/OR9Q
Lokacin kaɗa ƙuri'a a NigeriaHoto: AP

Majalisar dattijan Nigeria ta amince a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisa a watan janairu mai zuwa. A wani zama da ta yi a birnin Abuja a wannan larabar, majalisar ta albarkanci ƙudirin dokar da zata bayar da damar kwaskware jadawalin zaɓuɓɓukan na shekara mai zuwa.

sai dai dokar na bukatar amincewar takwararta ta wakilai da za ta yi zamanta kafin ƙarshen wannan nakon kafin ta fara aiki. Batun gudanar da zaɓen na daga cikin al'amuran da suka fi ɗaukar hankali a tarayyar ta Nigeria musamman ma bayan rantsar da komishinon hukumar zaɓe mai zaman kanta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Ahmed Tijjani Lawal