1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SABON KUNDIN TSARIN MULKIN IRAQ

JAMILU SANIMarch 8, 2004
https://p.dw.com/p/BvlS
A kasar Iraqi yau litinin dukanin yan majalisar zartaswar da Amurka ta nada su 25,suka rataba hanu kann sabon kundin tsarin mulkin kasar a wani biki da aka gudanar a birnin Bagadaza,duk kuwa da cewa karo biyu ke nan ana dage zaman rataba hanu kann sabon kundin tsarin mulkin na kasar Iraqi.

Yan majalisar zartaswar Iraqi su 25 karkashin shugabancin shugaban wanan majalisa Mohammed Bhar a-ulum suka rinka zuwa daya bayan daya sun sanya hanu kann sabon kundin tsarin mulkin na kasar Iraqi a gaban manyan baki da suka halarci wanan biki,ciki kuwa har da kantoman Amurka a Iraqi Paul Bremer.

A lokacin da ake gabatar da jawabia tun ma kafin a fara sanya hanu kann sabon kundin tsarin mulkin na Iraqi,dukanin yan majalisar zartaswar gwamnatin Iraqi sun yaba da irin wanan cigaba da aka samu,inda shi kansa shugaban wanan majalisa Uloom ya baiyana rataba hanun da yan majalisar zartaswar Iraqi suka amince su yi kann sabon kundin tsarin mulki,a matsayin baban abin tarihi ga alumar kasar Iraqi baki daya.

Bugu da kari Uloom din dai ya baiyana rataba hanu kann sabon kundin tsarin mulkin na Iraqi,a matsayin wani sabon ginshiki da zai samar da gwamnati irin ta democradiya a Iraqi wace kuma zata mutunta hakokin bil adama. A nasa bangarin kantoman Amurka a kasar Iraqi Paul Bremer,ya baiyana cewa koda yake ba kowa daga cikin yan majalisar zartaswar ta Iraqi suka sami kaiwa ga biyan bukatar da suke bukata cikin wanan sabon kundin tsarin mulki da aka rataba hanu kansa yau litinin ba,to amman kuma hakan na bisa tsarin da ake bi wajen shimfida mulki irin na democradiya.

An dai fara gudanar da wanan biki na sanya hanu kann sabon kundin tsarin mulkin kasar ta Iraqi ne da karatu daga alkurani mai girma. An dai bayana sanya hanu kann sabon kundin tsarin mulkin na Iraqi a matsayin wani baban cigaba da aka samu a yankin gabas ta tsakiya,wanda kuma ake ganin zai taimaka wajen baiwa alumar Iraqi yancin fadin albarkacin bakin su tare kuma da baiwa mata yanci. Tun ranar talatar data gabata aka dage bikin rataba han kan sabon kundin tsarin mulkin na Iraqi,bayan da aka fuskaci wasu hare hare na ta'adanci a wasu masalatai na yan shiite dake garin Karbala da kuma birnin Bagadaza. A nasa bangaren shugaban musulmi yan shiite na Iraqi Ayatollah Ali Sistani,ya baiyana sabon kundin tsarin mulkin da aka rataba hanu kansa a yau litinin da cewa zai kara jefa Iraqi cikin hali na kaka na ka yi.
A chan kuma kasar Iran alumar kasar sun nuna cikaken goyon bayan su tare da sanya albarka kann sabon kundin tsarin mulkin Iraqi na wucin gadi da yan majalisar zartaswar kasar da gwamnatin Amurka ta nada suka rataba hanu a kansa,inda suka baiyana wanan cigaba da aka samu da cewa mataki ne na da zai taka muhimiyar rawa wajen mika ragamar mulki ga yan asalin Iraqi.