1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici a gabashin Jamhuriyar Demukiradiyyar Kongo

January 22, 2006
https://p.dw.com/p/BvBC

Wani kazamin fada da ya barke tsakanin sojojin gwamnati da ´yan tawaye a gabashin kasar JDK ya tilasta dubban mutane tserewa daga yankin. Wani wakilin dakarun MDD a yankin ya fadawa kamfanin dilancin labarun Reuters cewa sama da mutane dubu 50 sun tsere daga gidajensu, yayin da wasu dubu biyu suka tsere zuwa cikin Uganda. Su dai ´yan tawayen dake karkashin jagoranci wani tsohon hafsan sojin kasar, na adawa da shirin wanzar da zaman lafiya wanda ya tanadi gudanar da zaben gama gari a fadin kasar ta Kongo a cikin watan afrilu.