1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici ya barke a gabashin Kongo

November 26, 2006
https://p.dw.com/p/BuaE
Wani sabon fada ya barke a gabashin JDK tsakanin sojojin gwamnati da ´yan tawaye dake karkashin jagorancin tsohon hafsan soji Janar Laurent Nkunda. Gidan radiyon France International ya rawaito cewa an yi fadan ne a kusa da da garin Sake dake kan iyaka da Rwanda. Akalla sojoji 7 da farar hula daya aka kashe a wani harin da dakarun Janar Nkunda suka kai jiya asabar wanda shi ne irinsa na farko cikin wata daya. MDD ta ce sojojinta sun yi musayar wuta da ´yan tawaye. A halin da ake ciki dubban mazauna yankin sun tsere daga fadan da ake yi a garin an Sake.