1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Sabon rukunin 'yan kasuwa a Tanzaniya

Ahmed Salisu
January 11, 2017

A kokarin ganin ta tallafa wa mata don dogaro da kansu ta hanyar yin sana'o'i, wata mata a kasar Tanzaniya mai suna Shekha Nasser ta bude makarantar horas da mata musamman ma wadanda ke da karamin karfi.

https://p.dw.com/p/2VcSP
Kenia Nairobi Perücken für Krebspatienten
Hoto: DW/A. Wasike

Tanzaniya dai na daga cikin kasashen Afirka da al'ummarta ke karuwa cikin hanzari sai dai da dama daga cikin wadannan mutane musamman mata na fama da rashin aikin yi. Wannan ne ya sanya Shekha Nasser ganin dacewar bada gudumawarta wajen sama wa irin wadannan mata aiki ko sana'a da za su yi dogaro da kansu maimakon jiran sai an dauko an basu, kamar yadda ta yi bayani.

 "Ina da kasuwanci wanda ke samun bunkasa amma kuma mata da yawa ba su da aikin yi, wasunsu ma basa iya cin abinci fiye da sau daya a rana. Ina da kayan da zan iya basu su sayar don su samu wani abu. Hakan zai taimaka mana wajen bunkasa tare."

Shekha dai na saye da mayuka ne na gyaran jiki da kuma na gyaran gashi wanda takan ba wa mata a farashi mai rahusa don su sayar da nufin samun wani abu a kai. A share guda kuma ta girka wata makaranta don koya wa mata gyaran jiki da kuma gyaran gashi don in sun kammala su samu damar bude gidaje na gyaran jiki ga 'yan uwansu mata. A ciki wannan shekara kadai mata kimanin 200 ne suka samu horo a wannan makaranta da ke birnin Dar-es-Salam.

Brisk trade in Zambia in women's hair
Mata masu iya dogaro da kai saboda sana'ar hannuHoto: DW/C. Mwakideu

"Wannan masana'anta ce da ake juya miliyoyin daloli amma kuma maza ne suka kankane ta musamman ma kasuwancin mayuka da mata ke amfani da su wanda ake shigo da su kasar nan. Sai dai kuma ko kusa ba sa tallafa wa mata ta hanyar horas da su."

Sanya mata cikin harkar kasuwanci don dogaro da kai

Wannan rashin damawa da mata din a wannan sana'a ta cinikayyar mayukan gyaran jiki na mata ya sanya Shekha Nasser horas da wani bangare na mata yadda ake yin kasuwancin wadannan hajjojin da ke kawo kudi sosai a kasar Tanzaniya. Domin samun nasara ta ganin matan sun shiga an dama da su sosai a harkar, Shekha ta bude wani kamfani na kanta da ke yin wannan kaya kuma ma tuni wannan tsari ya fara haifar da da mai idanu domin mutane irinsu Catherine Saninga da suka ci moriyar shirin na ta yin Allah san barka.

"Na ga banbanci matuka domin a baya a gida kawai nake a zaune tare da mahaifiyata. Abinda nake samu daa aikin da nake yi baya bai taka kara ya karya ba, amma yanzu na ga cigaba don ina da shagona na kaina, na gina gida kuma yanzu zan iya sanya dan da na haifa a makaranta. Ba abinda zan ce sai godiya ga Allah."

Wannan nasara da shirin Shekha Nasser ya samu na tallafa wa mata don samun abin dogaro da kai ya sanya matar yin kira ga wadanda suka ci moriyar tsarin da su tallafa wa sauran mata da ke cikin yanayi na rashin abin yi don ya kasance matan Tanzaniya da ma sauran sassan Afirka sun samu sukuni na dogaro da kai.