1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon Shugaban hukumar AU na da jan aiki

March 14, 2017

Sabon Hukumar Gudanarwa na kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya kama aiki a cibiyar AU da ke Adis Ababa. Tuni masana suka bayyana kalubalen da zai fuskanta a fuskar tsaro da hadin kan kasashen nahiyar.

https://p.dw.com/p/2Z9Uh
Äthiopien Debatte der Präsidentschaftskandidaten der Kommission der Afrikanischen Union
Hoto: DW/C. Wanjohi

Moussa Faki dan kasar Chadi ya karbi madafu ne daga hannun 'yar kasar Afirka ta Kudu Nkosazana Dlamini-Zuma, da a zamaninta ta yi kokarin daga likkafar mata a nahiyar Afirka. Sabon Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka ya hau kan karaga ne a daidai lokacin da nahiyar ke matukar bukatar gwanin da zai iya tinkarar al'amuran da ke matsa mata lamba ciki har da tsaro da bambance-bambancen siyasa dama kalubalen arziki.

Akwai rikice-rikice a wasu kasashen nahiyar, masalan rigimar Boko Haram da ta addabi kasashen yankin tafkin Chadi, da rigimar siyasa a kasar Sudan ta Kudu da Kwango, sai kuma matsalar fari da 'yunwa da ke Somaliya da wasu kasashen gabashin nahiyar. Masana irinsu Farfesa Umar Pate na jami'ar Bayero da ke Kano a Najeriya ya ce ayyuka ne masu bukatar tsayuwar sabon jagoran kungiyar ta AU.

Baya ma ga batun matsaloli da ke addabar nahiyar ta Afirka a yanzu, akwai ma irin kallon da manyan kasashe ke yi wa nahiyar na zama ta baya, inda ko a take-taken sabon Shugaban Amirka na yanzu Donald Trump, nahiyar bata cikin abin da hankali ka iya zuwa a gareta. Hasali ma sai da ya haramta wa 'yan kasashe irinsu Sudan da Somaliya da kuma Libiya shiga Amirka a yanzu. 

Äthiopien Treffen Afrikanische Union - Tschad Außenminister Moussa Faki
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/M. Wondimu Hailu

Akasarin kyamar a yanzu na kara tsanani sakamakon yadda ake ganin karuwar tserewa kasashensu da wasu Afirkawan ke yi don shigewa manyan kasashen na duniya. Abin da Professor Umar Pate ke cewa sabon jagoran kungiyar ta AU, ya yi nazari a kai.

Akwai ma wadanda ke ganin bukatar sabon jagoranicin na AU ya yi la'akari da bukatar sassauta zirga-zirga tsakanin kasashen kungiyar. Kamar yadda yake ra'ayi na Ambassador Issoufou Bashar, tsohon jami'an diflomasiyya da ke Jamhuriyar Nijar.

Wasu daga cikin matsalolin da ke cikin kungiyar da ake ganin za su iya tasiri ga ci bayanta su ne bambanci tsakanin kasashe masu amfani da harshen Ingilishi da kuma Faransanci da tsananin rashawa da cin hanci, sai kuma tsari na siyasa da akasari addini ki matukar tasiri a cikinsa.