1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shugaban Jamus?

June 3, 2010

Chiristian Wulff na jihar Lower Saxony ka iya zama mutumin da zai maye gurbin Horst Köhler

https://p.dw.com/p/NhRD
Christian Wulff mataimakin shugaban jam'iyar CDUHoto: picture alliance/dpa

Firimiyan jihar Lower Saxony dake arewacin Jamus Christian Wulff zai zama sabon shugaban ƙasar. Rahotanni sun yi nuni da cewa shugabar gwamnati Angela Merkel da shugaban FDP kuma ministan harkokin waje Guido Westerwelle da kuma shugaban jam'iyar CSU Horst Seehofer sun amince da Wulff mai shekaru 50 da zama mutumin da zai maye gurbin tsohon shugaban Jamus Horst Köhler wanda yayi murabus a ranar Litinin da ta gabata. Wadda da farko hankali ya karkata kanta a matsayin wadda za ta gaji Köhler wato ministar ƙwadago Ursula von der Leyen, ba ta samu goyon bayan jam'iyun guda uku ba. A lokacin da yake ba da jawabi bayan samun wannan rahoto, Christian Wulff dake zama mataimakin shugaban CDU cewa yayi.

"Ya kamata mutum ya dogara kan abin da ya sani, abin da na sani shi ne ni ne Firimiyan jihar Lower Saxony. Mai yiwuwa ni ma zan san abin da ke wakana amma a yanzu ba ni da wata masaniya akan wannan batu."

Ganin cewa jam'iyun dake mulki na da rinjaye a taron wakilan tarayya, zaɓan Wulff a matsayin magajin Köhler tabbas ne.

Su ma jam'iyu SPD da The Greens sun tsayar da tsohon jami'in kula da takardun bayyanan hukumar leƙen asirin tsohuwar Jamus ta Gabas Joachim Gauck a matsayin ɗan takararsu na neman muƙamin shugaban na Jamus.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Ahmed Tijani Lawal