1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon Shugaban Kasar Jamus

May 24, 2004

A jiya lahadi aka zabi Horst Köhler, tsofon darektan asusun ba da lamuni na IMF domin ya maye gurbin Johannes Rau a mukamin shugaban kasar Jamus

https://p.dw.com/p/BvjN
Zababben shugaban kasar Jamus mai jiran-gado Horst Köhler
Zababben shugaban kasar Jamus mai jiran-gado Horst KöhlerHoto: AP

Zaben ya gudana a cikin gaggawar da ba a taba ganin irin shigenta a zabubbukan shugaban kasar Jamus da suka gabata ba. A cikin awa daya da rabi aka kammala kammala zaben tare da kidayar kuri’un wakilai 1.204 da kuma ba da sakamakon da aka samu, inda Horst Köhler, tsofon darenktan asusun ba da lamuni na IMF ya samu rinjaye tare da kuri’u 604, a zagayen farko, a yayinda ita kuma abokiyar takararsa Gesine Schwan ta tashi ta kuri’u 589. Wannan sakamakon kuwa yayi nuni ne da cewar ba dukkan wakilan ‚yan Christian Union da FDP ne suka ba wa dan takararsu goyan baya ba, a maimakon haka sai suka goya wa ‚yan takarar SPD da the Greens baya. A cikin jawabinsa na farko Horst Köhler ya mika godiyarsa da zabensa da aka yi akan wannan mukami sannan yayi alkawari irin shigen wanda magabacinsa Johannes Rau yayi a lokacin da aka zabe shi misalin shekaru biyar da suka wuce wanda kuma ya zama shugaban kasar Jamus na farko da ya tabo maganar baki a cikin jawabinsa. Köhler ya ce:

Ina fatan zama shugaba ga dukkan Jamusawa. Shugaba mai magana da yawun dukkan mutanen dake zaune a nan kasar.

Köhler ya kara da cewar ba shakka duk kowa-da-kowa ya dokata ya ji ta bakinsa a game da manufofin garambawul, wadanda ba makawa game da su domin daidaita al’amuran tattalin arziki da zamantakewar jama’a a nan kasar. Bisa ga ra’ayinsa ana fama da tafiyar hawainiya a dukkan bangarori na rayuwa a Jamus. A nan take sabon shugaban na Jamus mai jiran gado ya tabo maganar kusantar juna da ake dada samu domin zama karkashin rumfa daya tsakanin dukkan sassa na duniya. Ya ci gaba da cewar:

Idan mun dauki nagartattun matakai akan manufa to kuwa ba shakka Jamus zata ci gajiya wannan kusantar juna da ake samu. Amma fa wajibi ne a daya bangaren a ba da la’akari ga sassan duniya dake cikin hali rabbana ka wadata mu ta yadda su amfana daga wannan ci gaba. Za a cimma biyan bukata ne kawai idan kasashe masu ci gaban masana’antu, abin da ya hada har da Jamus, suka canza take-take da kuma salon tunaninsu suka kuma bude kasuwanninsu ga kasashe masu tasowa.

Wajibi ne a kawar da tsoro a kuma fuskanci makoma tare da kwarin guiwa akan manufa.

A nata bangaren Gesine Schwan, ko da yake tayi asarar zaben, amma ta bayyana gamsuwarta da sakamakon da aka samu, musamman ma ganin yadda wasu daga cikin wakilan Christian Union da FDP suka ba ta goyan baya. Ta ce wannan sakamakon ya ba wa marada kunya, wadanda suka rika ikirarin cewar zaben shugaban kasar wani mizani ne da zai ba da haske a game da sabuwar alkiblar da Jamus zata fuskanta a siyasar kasar.