1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SPD Reaktionen

Awal, MohammadSeptember 8, 2008

An yi kira da haɗin kai tsakanin ´ya´yan jam´iyar ta SPD dake cikin gwamnatin ƙawance

https://p.dw.com/p/FDUa
Steinmeier ministan harkokin waje kuma ɗan takarar jam´iyar SPDHoto: AP

Bayan canjin shugabanci na ba zata da aka samu a cikin jam´iyar SPD a nan Jamus, an yi kira da a samu haɗin kai tsakanin ´ya´yan jam´iyar ta Social Democrat. Shugaban ɓangaren jam´iyar a majalisar dokokin tarayya Peter Struck ya ce yanzu lokaci ne da jam´iyar za ta fuskanci alƙiblar da ta sa a gaba.


A lokacin da ya ke mayar da martani bayan sauyin shugabanci a cikin jam´iyar ta SPD wadda ke cikin gwamnatin ƙawance da jam´iyun haɗin guiwa na CDU da CSU, shugabanta a majalisar dokoki ta Bundestag, Peter Struck ya ce abin da ska sa gaba shi ne buɗe wani sabon babi sannan ya yi kira da a kawo ƙarshen taƙaddamar da ke wanzuwa tsakanin ɓangarori daban daban na jam´iyar.


Ya ce "Ina ganin yanzu dukkan ´ya´yan jam´iyar ciki har da ´yan ɓangaren ra´ayin sauyi sun san cewa ya zama wajibi mu haɗa kawunan mu. Ba lokaci ne na yin wata muhawwara dangane da janye wani sashe na shirin sauye sauye na ajanda ta 2010 ba, domin tuni mun riga mun yi wannan canji a gun babban taronmu na birnin Hamburg."


Ita ma ´yar gani kashenin ra´ayin gurguzu kuma mataimakiyar shugabar SPD Andrea Nahles ta yi magana dangane da samun haɗin kai, tana mai cewa SPD za ta yi ƙarfi ne idan aka samu fahimtar juna da aiki da manufofinta.


Bayan murabus ɗin ba zata da shugaban SPD Kurt Beck ya yi a jiya Lahadi, a wani lokaci yau kwamitin gudanarwar jam´iyar zai naɗa tsohon shugabanta kuma tsohon mataimakin shugaban gwamnatin Jamus Franz Müntefering a matsayin sabon shugaban jam´iyar. Kafin a tabbatar da Müntefering a gun babban taron jam´iyar, ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier zai ci-gaba da jan ragamar jam´iyar. Steienmeier ɗin ne kuma zai tsayawa SPD zai ƙalubalanci Angela Merkel a zaɓen shugaban gwamnati da zai gudana a baɗi. Tuni Steinmeier ya ce a shirye ya ke tsayawa jam´iyar takara.


Ya ce:"Ina tabbatar muku da cewa ba zan tsaya takara ne a matsayin ɗan rakiya ba. Za mu yi aiki tuƙuru domin ganin SPD ta haye kan mulki a Jamus a cikin kwanaki 365 masu zuwa."


A lokacin da take mayar da martani dangane da sauyin shugabanci a jam´iyar ta SPD, shugabar gwamnati ´yar jam´iyar CDU, Angela Merkel ta yi suka game da abubuwan da suka janyo murabus ɗin na Kurt Beck ta na mai cewa ba su dace da manufofin jam´iyar dake matsayin ta al´uma ba. In da ta nuna damuwa game da ɓarakar dake cikin jam´iyar dake cikin gwamnatin ƙawance.


Ta ce: "Idan ka bi diddigin yadda aka zaɓi ɗan takarar na jam´iyar SPD za ka cewa ba a bi dokokin jam´iya irin ta al´uma ba, kuma wannan ya nunar a fili irin mummunar ɓarakar dake tsakanin ´ya´yan SPD."


Yanzu haka dai jam´iyun haɗin guiwa na CSU da CDU sun yi kira ga SPD ta su fito ƙarara ta nuna aniyar ci-gaba da kasancewa cikin gwamnatin ƙawance.