1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon tarihi a siyasar Jamus

October 10, 2005

Shugabar jam'iyar CDU, Angela Merkel zata zama sabuwar shugaban ghwamnati taraiya

https://p.dw.com/p/BvYz
Angela Merkel, zata karbi mukamin shugaban gwamnati
Angela Merkel, zata karbi mukamin shugaban gwamnatiHoto: dpa - Bildfunk

Jamus dai ta shiga wani sabon zamani a al’amuran ta na siyasa, bayan da aka zabi shugaban jam’iyar CDU, Angela Merkel ta zama shugaban gwamnmati ta farko mace a tarihin kasar. Bayan muhawara na makonni ukku, tun da aka gudanar da zaben majalisar dokokin taraiya, ranar goma sha takwas ga watan Satumba, manyan jam’iyun kasar, wato CDU da SPD sun daidaita a kann cewar Angela Merkel zata karbi mukamin shugaban gwamnati, inda zata gaji mai rike da mukamin ya zuwa yanzu, Gerhard Schroeder na jam’iyar SPD. Merkel ta fito ne daga yankin gabashin Jamus, kuma ta shiga harkokin siyasa sosai ne bayan sake hadewar kasar a shekara ta 1990.

To Frau Angela Merkel dai bata sami al’amura da sauki kamar yadda taso ba. A lokacin da ta shiga harkokin siyasa, har ma an rika kiran ta da junan yar kore ce, ko kuma yar lelen Kohl, saboda tsohon shugaban gwamnatin na Jamus, shine ya maida hankalin ganin Merkel, masaniya a fannin kimiya daga gabashin Jamus ta sami ci gaba a fannin siyasa. A matsayin ta na mace, gabashin Jamus, kuma yar darikar Protestant, tilas sai da tasha gwagwarmaya cikin jam’iyun hadin gwiwa na CDU da CSU. To amma a sakamakon dabaru da hangen nesa ta sami nasarar shimfida tarihin da ba’a taba samun kamar sda ba a kasar ta Jamus. Zata zama mace ta farko kann mukamin shugaban gwamnatin kasar Jamus. To sai dai wannan ci gaba da ta samu, bai zo mata cikin ruwan sanyi ba. Da farko bata sami karbuwa sosai ba, a tsakanin su kansu yan jam’iyar ta da sauran al’ummar kasa. Yar siyasa matashiya a wancan zamani, an dauka cewar bata da kwarewa ko kwarjinin da zasu jagorance ta ya zuwa ga kasancewa wata yar siyasa ta azo a gani a kasa. To amma Frau Merkel tace duka wadannan basu dame ta ba, burin ta shine ta ci gaba da kiyaye matsayin ta na siyasa da kuma fannoni masu muhimmanci da suka shafi siyasar. Tace:

Wadannan dai sune iyakacin abubuwan dake zuciya ta. Burin mu shine mu kiyaye sharuddan da suka shafi siyasa, mu kare democradiya da tsarin jari hujja mu kuma sami nasarar shawo kann kalubalen da wannan sabon zamani zai zo mana dasu.

Angela Merkel, wadda zata cika shekaru hamsin da daya a bana, an haife ta ne a Hamburg, amma ta taso ne a Templin a yankin Uckermark dake arewacin Berlin, yankin Jamus ta gabas. Mahaifin ta dai limamin kirista ne na darikar Protestant. Tayi nazarin ilimin Phisik a Leipzig, kuma tayi aiki a cibiyar bincike a yankin na gabashin Jamus. Bata shiga siyasa sosai ba, sai bayan rushewar kwaminisanci a yankin. Ta rike mukamin mataimakiyar kakakin gwamnatin democradiya ta farko a Jamus ta gabas, inda daga wnanan lokaci ta tsunduma sosai a al’amuran siyasa.

Shugaban gwamnati, Helmut Kohl ya nada ta kann mukamin ministan mata da matasa, sa’annan daga baya ta karbi ma’aikatar kare muhalli. Jaridu sun rika kwatanta ta a matsayin yar lelen Kohl, saboda wai wadannan mukmai ta same su ne tare da kariya daga shugaban gwamnatin. A bayan da Helmut Kohl yayi murabus, magajin sa na dan gajeren lokaci a matsayin shugaban jam’iyar CDU, Wolfgang Schaeuble ya nada Merkel a matsayin janar sakatare na jam’iyar. Sakamakon babban abin kunyar nan na kin biyan haraji da jam’iyar CDU ta fuskanta, yan jam’iyar sun nemi Frau Merkel ta karbi shugaban cin ta, inda suka nemi ta kafawa jam’iyar sabopn tushe.

Yan jam’iyar ta CDU da dama a wancan lokaci, sun yi yi zaton cewar da zaran Angela Merkel ta kammala aikin kawar da wadandake neman bata sunan jam’iyar, ta kuma dora ta kann sabuwar hanya, kawar da ita ba zai zama abu mai wahala ba, saboda bata da kwarewa, kuma gashi daga gabashin Jamus ta fito. To amma sannu a hankali Frau Merkel ta shiga nunawa masu neman kawar da ita cewar ita ma mace ce mai kamar maza, saboda haka ta kara karfin rikon ta kann shugaban jam’iyar ta CDU. Frau Merkel, ta janye daga aiyukan rashin gaskiya da aka zargi Helmut Kohl da aikatawa, amma daga baya ta taimaka domin sulhunta tsakanin tsohon shugaban gwamnatin da yan jam’iyar sa.

Frau Merkel dake da aure da masanin ilimin hada magunguna, Prof. Joachim Sauer tana sane da irin wahalolin dake tattare da aikin da zata karba, idan ta sami nasarar zaben majalisar dokoki da aka yi a watan jiya. Duk da haka, bata janye ba, amma a maimakon haka, tace daidai take da duk abokan adawar ta na siyasa. Tace:

Mune muka fi karancin bunkasar tattalin arziki a Turai. Ba kuwa wani abu ya kawo haka ba, sai rashin tsari mai kyau a al’amuran siyasa na cikin gida. A shekara ta 2000, mun kasance da rarar kudi Euro miliyan dubu ashirin da ukku a bangaren kyautata jin dadin zaman jama’a. A yau, babu sauran wnanan kudi. Gwamnatin dake kann mulki ta lalata wannan kudi. Wahnnan dai shine gaskiyar al’amarin.

A shekara ta 2002, Angela Merkel ta baiwa shugaban jam’iyar CSU, Edmund Stoiber damar tsayawa takarar neman mukamin shugaban gwamnati. Ko da shike Stoiber bai sami nasara ba, abin da ya kara karfafa matsayin Merkel. A bayan mukamin ta na shugaban jam’iyar CDU, ta kuma karbi shugabancin wakilan jam’iyun CDU da CSU a majalisar dokokin taraiya.

A zaben da aka yi ranar sha takwas ga watan Satumba, Frau Merkel ta sami sabuwar damar tsayawa a takarar neman mukamin shugaban gwamnati. Ko da shike bata sami kuri’u fiye da kashi talatin da biyarda digo tara cikin dari ba, amma an sake zaben ta kann mukamin shugabancin jam’iyar, kuma a karshe ta cimma burin ta na kasancewa mace ta farko da zata rike mukamin shugaban gwamnati a tarihin Jamus.