1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin fyade a Bangui

Yusuf BalaFebruary 16, 2016

Wani jami'in MDD ya fada wa manama labarai cewa cikin wadanda aka aikaitawa lalatar har da kananan yara.

https://p.dw.com/p/1Hvzc
Französische Soldaten in der Zentralafrikanischen Republik
Hoto: AFP/Getty Images/P. Pabandji

Majalisar Dinkin Duniya ta shiga wani sabon aikin bincike na zargin aikata laifukan fyade da dakarun wanzar da zaman lafiya nata suka aikata a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wani abu da aka saba zargin dakarun majalisar da aikatawa kamar yadda mai magana da yawun majalisar ya bayyana a ranar Litinin.

Farhan Haq ya ce tuni tawaga daga kasar Kwango ta isa kasar ta jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dan gudanar da aikin bincike kan sabon zargin aikata mugun aikin da ke ci gaba da rage kimar Majalisar Dinkin Duniyar.

Sai dai mista Haq bai bada cikakken bayani ba kan zargin, da wani jami'i a majalisar ya fada wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa cikin wadanda aka aikaitawa lalatar har da kananan yara.

A farkon wannan wata dai an sami dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniyar bakwai da aikata wannan laifi da aka aikatawa mata da kananan yara kamar yadda kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch.