1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar dangantakar Amurka da kawayenta a nahiyar Turai

February 9, 2005

A ziyarar da take ga kasashen Turai sabuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice ta yi kiran bude wani sabon babi ga dangantakar Turai da Amurka

https://p.dw.com/p/BvdI
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza rice
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza riceHoto: AP

A dukkan kasashen Turai da ta kai musu ziyara, kama daga Polen zuwa Italiya da Faransa da Belgium, a dukkan wadannan yankuna sakatariyar harkokin wajen Amurkan Condoleeza Rice tayi musu tayin tsaffin manufofinta a cikin wata sabuwar suffa. Ga alamu kuma kwalliya ta mayar da kudin sabulu dangane da wannan mataki nata domin yayi tasiri sosai da sosai a zukatan kasashen na Turai. Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika sun sha jinin jikinsu suna masu kada kawuna lokacin da Condoleeza Rice ke bayanin cewar wai a yanzu wata kyakkyawar dama ce ta samu domin dinke barakar da ta samu tsakanin kasashen Turai da Amurka dangane da yakin Iraki. Bayan lafuzza na sulhu da aka ji daga bakinta sakatariyar harkokin wajen Amurkan ba ta yi wata-wata ba wajen bayyana wa kawayenta cewar fadar mulkin ta White House na fatan samun kyakkyawan hadin kai daga kasashen Turai. A nasu bangaren kasashen na Turai sun yi watsi da gaskiyar cewa ita Condoleeza Rice, a matsayinta na mashawarciyar shugaban kasa akan al’amuran tsaro, ita ce ta ja akalar manufofin Amurka dangane da kasar Iraki. Kazalika ita ce ta nemi ladabtar da kasar Faransa da yin ko oho da Jamus, bayan da sojojin Amurka suka mamaye Iraki. A yanzu sai ga shi an wayi gari, Condi, kamar yadda shugaba George Bush ke kiranta, tana mai neman hadin kai daga kasashen Turai akan wani mataki na gaba. Babu daya daga cikin kasashen da ta fito fili da kalubalance ta, duk kuwa da kasancewar bayanin da tayi na cewar Amurka, har kwanan gobe tana kan bakanta na wanzar da abin da ta kira wai ‚yantar da talakawa daga mulkin fir’asunanci da kama karya a nahiyoyin Asiya da Afurka da kuma kasar Cuba, abu ne da ka iya yin mummunan tasiri akan nahiyar Turai. A yanzun dai an yi shiru ne ana sauraron bayanin da sakataren tsaron Amurka Ronald Rumsfeld zai yi wa takwarorinsa na kungiyar NATO a game da ainifin abin da Amurkan ke bukata daga garesu. A wannan bangaren ita Condoleeza Rice bata yarda ta shafa wa kanta kashin kaza ba. Ita dai tana taka rawa ne ta nuna sassaucin manufofi a yayinda shi kuma Rumsfeld ke a matsayin wani uba mai tsawata wa ‚ya’yansa tare da neman ganin kasashen Turai sun kara yawan sojojinsu a Afghanistan da kuma yawan jami’an ba da horo da karin makamai ga kasar Iraki. Bayan wannan take-take na share fage, ba shakka shuagabannin kasashen Turai zasu gurfana a gaban shugaba George W. Bush suna masu yi masa maula, a lokacin ganawar da zasu yi nan da makonni biyu masu zuwa. Irin alkiblar da za a fuskanta dangane da kasashen Iran da China ka iya zama babban zakaran gwajin dafi dangane da sabuwar dangantakar ta kasashen Turai da Amurka.