1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar Dokar Deutsche Welle

October 29, 2004

A jiya alhamis ne majalisar dokoki ta Bundestag ta albarkaci sabuwar dokar DW dangane da yawan abin da za a rika kasafta wa tashar a kowace shekara

https://p.dw.com/p/Bvf2
Majalisar Dokokin Jamus ta Bundestag
Majalisar Dokokin Jamus ta BundestagHoto: AP

Ba tare da wata hamayya ba majalisar dokokin Bundestag ta albarkaci sabon kundin na dokar ayyukan tashar Deutsche Welle. Wannan matakin na da nufin karfafa goyan baya ga shirye-shiryen da tashar ke yadawa zuwa sassa dabam-dabam na duniya ta gidajen rediyo da telebijin da kuma yanar gizo. A lokacin da take bayani game da haka karamar minista mai kula da al’amuran al’adu da kafofin yada labarai a fadar shugaban gwamnati, Christina Weiss tayi nuni da cewar ayyukan DW ba shirye-shirye ne na son kai ba, kuma ba kawai sun danganci yada sahihan labarai ba ne, kazalika wata kafa ce ta wayar da jama’a akan dukkan bangarori na al‘adun Jamus. a saboda haka wannan sabuwar doka take da muhimmanci matuka ainun a manufofin kyautata dangantakun al’adu. A nasa bangaren Bernd Neumann daga ‚yan hamayya na Christian Union yayi korafin cewar gwamnati ba ta wakilta wani kwararren masani mai zaman kansa da zai binciko ainihin yawan kudaden da DW ke bukata domin tafiyar da ayyukanta salin-alin ba tare da tangarda ba. Domin kuwa a karkashin dokar, majalisar Bundestag na da ikon sake bitar abin da za a kasafta wa tashar ta DW a kowace shekara. Shawarar farko da aka gabatar dangane da yawan abin da za a rika kasafta wa tashar, ma’aikatar kudi ta tarayya ta sa kafa tayi fatali da ita, bisa ikirarin cewar in har an biya wa DW wannan bukata, to kuwa ba shakka ragowar kafofin dake samun tallafi daga gwamnati zasu nemi yin koyi da ita. Neumann ya kalubalanci wannan batu, inda yake cewar:

Tashar yada labarai irin shigen DW ba za a iya kwatanta ta da sauran kafofi na gwamnati ba, saboda ayyukanta sun banbanta da na sauran mahukunta. Ita tasha ce ta yada labarai kuma ma’aikatanta ‚yan jarida ne dake bakin kokarinsu wajen biyayya ga sharuddan da aka shimfida musu na ba da fifiko wajen tsage gaskiya akan dukkan abubuwan dake faruwa ba tare da nuna son kai ba.

Ita dai DW an kirkiro ta ne tun misalin shekaru 50 da suka wuce, inda a yanzu haka take yada shirye-shirye na rediyo a cikin harsuna 30, sai kuma shirin telebijin a cikin harsuna uku a daura da shirye-shirye ta yanar gizo a na’ura mai kwakwalwa. Gaba daya tana da ma’aikata 1500 daga kasashe 60 an kuma tanadar mata da kasafin kudi na Euro miliyan 260 dangane da shekarar kudi mai kamawa.