1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar dokar 'yan gudun hijira a Denmak

Gazali Abdou TasawaJanuary 26, 2016

Sabuwar dokar wacce majalisar dokokin kasar za ta sanya wa hannun a yau ta kunshi wasu matakai wadanda ke da burin karya kuzarin duk 'yan gudun hijrar da ke hankoron zuwa kasar da nufin samun mafaka.

https://p.dw.com/p/1Hjrd
Flüchtlinge Slowenien
Hoto: DW/A. Langley

A yau ne majalisar dokokin kasar Denmak ke sanya hannu kan wani daftarin dokar tsarin kula da 'yan gudun hijira a kasar mai cike da cecekuce. Sabuwar dokar dai ta kunshi wasu matakai wadanda ke da burin karya kuzarin duk 'yan gudun hijrar masu hankoron zuwa kasar da nufin samun mafaka.

Matakan da dokar dai ta kunsa sun hada da bai wa 'yan sandar kasar izinin bincikar kayan bakin dama kwace kudi tsaba da yawansu zai haura Euro dubu daya da 340, dama kuma kadadorin da suka kai darajar wannan kudi da za a samu a hannun 'yan gudun hijirar.

Tuni dai wannan mataki ya soma fiskantar suka daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam wadanda suka soma danganta shi da irin matakin karbe kadarorin Yahudawa da milkin 'yan Nazin kasar jamus ya yi amfani da shi a wancan lokaci.