1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnati a Irak

November 25, 2010

An rantsar da Nuri al-Maliki a matsayin saban Firayim Ministan Irak bayan wata da watani na taƙƙadamar siyasa

https://p.dw.com/p/QHwr
Nuri al-MalikiHoto: AP

A yau ne aka rantsar da Frime Minista mai ci Nuri al Maliki a matsayin Frime Ministan ƙasar Irak a hukunce,  a ka kuma gayyace shi ya kafa sabuwar gwamnati . Wannan gayyata da Maliki ya samu daga shugaban ƙasa Jalal Talabani, ta zo ne sakamakon wata yarjejeniya da su ka ƙulla domin waraware rikicin wanda ya ci zaɓe, a zaɓukan ƙasar da aka gudanar a watan Maris da ya gabata, wanda kuma aka ɗauki tsawon watanni takwas ana yi.

A yanzu haka dai an bayyana wa ɓangarorin siyasar ƙasar, yadda za su gudanar da yarjejeniyar samun ministoci a sabuwar gwamnatin da za'a girka.

Banda Maliki, da ya hito daga ɗarikar Shi'a, da shugaban ƙasa Talabani wanda baƙurde ne, yarjejeniyar ta ambaci wani balarabe ɗan sunni, a matsayin kakakin majalisar dokokin ƙasar.

Tsohon Firayima Ministan ƙasar, Iyad Allawi zai jagoranci hukumar kula da tsaro.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Umaru Aliyu