1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnati a Ivory Coast

Zainab A.MohammedApril 10, 2007
https://p.dw.com/p/Btvp
Shugaba Laurent Gbagbo
Shugaba Laurent GbagboHoto: AP

Shugaban rundunar kiyaye zaman lafiya na mdd dake kasar Ivory Coast,ya bayyana cewa nan bada jimawa ba dakarun zasu fara ficewa daga yankunan kan iyakokin yankin arewaci dake hannun yan tawaye da kuma kudanci dake karkashin ikon gwamnatin kasar.

Wannan mataki da ayarin kiyaye zaman lafiya suka dauka ya biyo bayan rattaba hannu a yarjejeniyar da bangarorin biyu sukayi ne,dangane da sulhunta kan kasar baki daya.

General Fernard Marcel Amoussou dake jagorantar rundunar kiyaye zaman lafiya na mdd kimanin 7,800 dake Ivory Coast din ya bayyana cewa,a ranar goma sha shida ga wannan wata ne sojojin zasu fara janyewa.

Tun dai bayan yukurin kifar da gwamnatin kasar nedai karamin yakin basasa ya barke a wannan kasa a shekarata 2002,rikicin daya dare kasar zuwa yankuna biyu.

Cikin shekaru hudun da suka gabat dai yankin arewacin kasar ya kasance a hannun yan adawa akarkashin jagorancin Guillaume Soro,kafin acimma sulhu a watan daya gabata ,yarjejeniyar da ta samar da hanyar da kafa gwamnatin hada kan kasa wadda shugaban yan adawan zai kasance prime minista.

Tunda farko dai jamian sojin kasar faransa sun sanar dacewa 500 daga cikin dakarunsu 3,500,zasu fara janyewa daga cikin kasar ta Ivory coast.Dakarun mdd na jibge ne a tsakanin yankunan guda biyu,watau arewaci da kuma kudancin kasar ta Ivory coast.Adangane da hakane commandan rundunar mdd Amoussou ya bayyana cewa zasu mikawa dakarun gwamnatin kasar ,alhakin kulawa da harkokin tsaro a wannan yanki da zasu janye.

A kareshen makon daya gabata nedai shugaba Laurent Gbagbo ya sanar da nadin sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a karkashin shugaban kungiyar yan adawan kasar Guillaume Soro,batu dazai ga sake hadewan kawuwan wannan kasa dake yankin yammacin Afrika mai arzikin koko.

Akweai kyakkyawan fatan cewa,wannan yarjejeniyar da aka cimma zai taimaka wajen dunke dukkan barakar da kasar ta Ivory Coast ta kasance aciki musamman na yakin basasa da aka gwabza tsakanin 2002-2003,bayan gazawan kasashen ketare wajen cimma sulhunta kan kasar.

Kakakin sabbin dakarun sojin Mr Soro Sidiki Konate ,ya bayyana cewa manufofin wannan gwamnati na hadin kan kasa a bayyana suke,dole ne gwamnatin ta warware matsalar wayan nene yan kasa ,da kuma sake ginin rundunar tsaronta ,tare da batun shirya zaben kasa baki daya.

An samu matsaloli na kabilanci sakamakon kwararn yan kasar ta Ivory,da samun yancin kanta daga faransa a 1960.