1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar gwamnatin Israi´ila zata sake fasalta kan iyakokinta

May 4, 2006
https://p.dw.com/p/Buzg

A wani jawabin bayyana manufofin gwamnatinsa da ya yiwa majalisar dokokin Isra´ila, FM rikon kwaryar Ehud Olmert ya gabatar da wani sabon shiri game da kan iyakokin Isra´ila. Olmert ya ce yanzu ya zama wajibi kasar ta Bani Yahudu ta yi watsi da daidaikun kananan matsugunan Yahudawa dake gabar Yamma da Kogin Jordan. To amma zata ci-gaba da iko da manyan unguwannin yahudawa ´yan kakagida. Olmert ya kara da cewa zai fi son ya cimma wata yarjejeniya da Falasdinawa ta hanyar yin shawarwari, to amma idan hakan ya ci-tura, to zai yi gaban kan shi wajen kirkirowa Isra´ila sabbin kan iyakoki. Olmert ya yi wannan jawabi ne jim kadan gabanin a rantsad da majalisar ministocinsa wadda ta kunshi ´ya´yan jam´iyarsa ta Kadima da ta Labour da kuma wasu kananan jam´iyu guda biyu.